Fargabar matsalar karancin abinci a Gabashin Najeriya 


Majalissar dinkin Duniya  ta yi gargadin cewa akwai fargabar matsalar karancin abinci da ake fama da ita a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ta nunka zuwa gida biyu nan da wata daya. 
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai fargabar matsalar karancin abinci da ake fama da ita a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ta nunka zuwa gida biyu nan da wata daya, sabili da matsalar rikicin Boko Haram da ta tawaye da kuma ta  tattalin arziki da kasar take fuskanta.

Bettina Luescher mai magana da yawan hukumar kula da ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya wato PAM ce ta sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai a wannan Jumma’a a birnin Geneva inda ta bayyana cewa rikicin Boko Haram ya jefa mutanen sama da miliyan uku cikin matsalar karancin abinci a yankin na Arewa maso gabashin kasar, amma kuma matsalar na iya shafar nan gaba kadan mutane miliyan biyar da rabi sabili da matsalar tattalin arzikin da Najeriyar ta shiga a dalilin faduwar darajar man fetur a kasuwar duniya.

You may also like