Kungiyar Kare Hakkin Bil-adama ta ‘Human Rights Watch ‘ tace kasar Kamaru ta dawo da yan Najeriya 100,000 dake gudun hijira gida, a kokarin da take na dakatar na hana bazuwar rikicin Boko Haram a kasar.
A wani rahoto da kungiyar ta fitar yau Laraba tace dawo da mutanen gida ya saba da rokon da hukumar kula yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tayi na kada a mayar da mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya har sai “yanayin tsaro da kuma hakkin dan adam ya inganta dai-dai misali a yankin.”
Rahoton yace akwai yiyuwar mutanen zasu fuskanci wani sabon rikici.
Hukumar dake binciken zarge-zargen cin zarafin bil-adama a duniya baki daya tace an rubuta rahoton ne bayan da hukumar ta tattauna da yan gudun hijira 60.
Ta kara da cewa sojojin kasar Kamaru sun azabtar da yan gudun hijirar tare da cin zarafinsu a wasu lokutan ma har da hanasu isa sansanin yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya