Fasanjoji sun kama dan fashi da makami 


mai safarar makamai da aka kama a hanyar Zamfara

Yan sanda a jihar Benue sun nuna wani da ake zargi da aikata fashi da makami wanda fasinjoji suka kama bayan da ya kwace musu kayayyaki.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, Moses Joel Yamu, ya ce Terngu Nabe, da kuma wasu mutane biyu da ake nema sun tsare fasinjoji a  daren ranar Laraba a kan titin Abua dake karamar hukumar Baruku.
Yamu ya ce yan fashin su uku sun samu nasarar aikata fashin yayin da daya daga cikin fasinjojin yayi ta maza ya kama Nabe ta baya.

Ya ce a wannan lokacin da ragowar yan fashin suka ga haka sai suka gudu cikin daji yayin da ragowar mutanen cikin motar suka fito suka rike Nabe har sai da yan sanda sauka iso wurin.

Nabe da yake zantawa da jaridar Daily Trust ya amince da aikata laifin inda yace wannan ne karonsa na farko bayan da yadade yana kin amsa gayyatar ɗan uwansa na suje su aikata fashi da makami.

You may also like