Dandazon taron jama’a ne suka cika Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Asabar lokacin da ministan ma’adanai, tama da karafa, kuma tsohon gwamnan jihar, Kayode Fayemi,ya kaddamar da takararsa ta sake neman darewa kujerar mulkin jihar.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC, ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar a cikin watan Yunin wannan shekara.
Da yakewa magoya bayansa jawabi Fayemi wanda ya mulki jihar tsakanin shekarar 2010 ya zuwa 2014 ya ce yana da aiyukan da bai kammala ba gidan gwamnatin jihar.
Ya kuma ci alwashin tuhumar gwamn, Ayodele Fayose, gwamnan dake mulkin jihar a yanzu inda ya zargeshi da barnatar da kudaden jihar.