Kayode Fayemi, ministan ma’adanai da habaka karafa ya sauka daga mukaminsa.
Ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da yake ganawa da yan jaridu a Abuja.
Fayemi shine dan takarar jam’iyar APC a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a gudanar ranar 14 ga watan Yuni, bayan da ya samu kuri’u mafiya rinjaye a zaben fidda gwani na jam’iyar da aka sake gudanarwa.
A wancan lokacin, Fayemi ya bayyana cewa mako guda ya rage masa ya cigaba da aiki a matsayin minista bayan nan kuma zai mayar da hankali kan lashe zaben kujerar gwamnan jihar.
Fayemi ya kasance gwamnan jihar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2014 inda ya yi rashin nasara a hannun gwamna mai ci a yanzu Ayo Fayose.
A wannan karon Fayemi zai yi takara yan takarkaru da dama ciki har da dan takarar jam’iyar PDP wanda shine mataimakin gwamnan jihar, Kolapo Olusola dake samun goyon bayan gwamna Fayose.