Ayo Fayose gwamnan jihar Ekiti a ranar Alhamis ya ziyarci jihar Benue domin jajantawa mutanen jihar kan rikici tsakanin fulan makiyaya da kuma manoma.
Sama da mutane 80 aka kashe a jihar cikin shekara da muke ciki kaɗai.
Gwamnan jihar, Samuel Ortom tare da mukarrabansa su ne suka tarbi Fayose wanda shine shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP.
Fayose ya yi addu’a a kabaruruwan mutane 73 da aka kashe cikin watan Janairu.
Ziyarar ta Fayose na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya kai makamanciyar wannan ziyara.