Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya sake yin kira ga Shugaba Buhari kan ya yi murabus inda ya dora alhakin tabarbarewar harkokin tsaro da na tattalin arziki a kan rashin kwarewar Shugaban.
Gwamnan ya ce, a halin yanzu farashin fetur ya kai kusan Naira 180 yayin da basussukan da ake bin Nijeriya ya haura Naira Tiriliyan 20 daga Naira Tiriliyan 12 a 2015. A bangaren tsaro kuwa, gwamnan ya jaddada cewa rashin tsaro ne ya janyo Boko Haram suka samu nasarar sake arcewa da wasu dalibai a daidai lokacin da ake fafitikar yadda za a kwato sauran ‘yan Matan Chibok.