Ficewar Atiku ba zai shafi APC ba – Oyegun


Cif John Odigie Oyegun  shugaban jam’iyar APC na kasa ya tabbatarwa da yan jam’iyyar cewa ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar daga jam’iyar ba zai shafe ta ba ta kowanne ɓangare.

Ya bada wannan tabbacin a Abuja lokacin da ƙungiyar tsofaffin shugabannin mazabu, kansiloli da kuma ciyamomi suka ka masa ziyara a Abuja.

“kada wani yaji tsoron cewa fitar tsohon mataimakin shugaban kasa zai kai ga fitar mutane da yawa.

” Kada kuji tsoron cewa za a samu fitar mutane da yawa.

“A zahirin gaskiya sai aka samu akasin haka domin karfin jam’iyar kullum dada karuwa yake.”

Shugaban na APC ya kuma kara tabbatar da cewa ficewar ta Atiku baza ta jawo ficewar mutane masu yawa ba kamar yadda wasu mutane ke hasashe.

Ya jaddada cewa babu wata jam’iya da ba ta fama da rikici kamar APC  ya kara da cewa ko jam’iyar PDP har yanzu fama take da rikici kan wa zai shugabance ta.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like