Fim guda goma mafi-kyau na Kannywood a 2016


A 2016 an saki fim masu yawa sossai a Kannywood. Idan ba ku samu lokacin kallon yawancin fim na Kannywood ba, mun kawo muku shawara akan shirin da ya fi shaʼawa.

Ƴan jaridan Arewa24news masu kula da wasan kwaikwayo sun lissafa bidiyo goma waɗanda sun fi daɗin kallo. Waɗanan fim sun ƙunshi salon wasa daban-daban kaman wasan soyyaya, wasa mai ban shaʼawa da kuma wasa mai ban dariya.

afra

1. Afra

Manyan Ƴan wasa cikin Afra su ne Adam A Zango, Fati Washa, Rabiu Rikadawa da Tijjani Faraga. Darektan wasa shi ne Nura M Inuwa.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

ahmad

 

2. Ahmad

Cikin wannan shiri, akwai Ibrahim Maishunku, da Aminu Sheriff. Wannan wasa mai ban shaʼawa, ya shafi abubuwan da suka faru a yayin da an sace ɗiyar wani babban ɗan siyasa. Yakubu M Kumo shi ne marubucin wasa, kuma MuʼAzzam Idi Yari shi ne darekta.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

 basaja-gidan-yari

3.Basaja Gidan Yari

Idan kana shaʼawan wasan da ya shafi aikace-aikacen laifuka da bincike-binciken laifuka, ka ƙokarta ka kalla “Basaja Gidan Yari”. Babban Ɗan Wasan Kwaikwayo Adam A Zango shi ne darektan wannan wasa.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

dan-kuka

 

4. Ɗan Kuka

“Ɗan Kuka” wasa ne na ban dariya wanda Adamu Zango ya yi. Wannan wasa ya shafi dubarun wani baƙauye. Ado Gwanja yana cikin wannan shiri.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

fasbir

 

5. Fasbir

A cikin wasa mai suna “Fasbir”, akwai ƴan wasa na gaban goshi kaman Ali Nuhu, Faraga, Tanimu Akawu da Ramadan Booth.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

iyalina

 

6. Iyalina

“Iyalina” wasa ne mai kyau wanda Yaseen Auwal shine darektan wasa. A cikin wannan wasa, za ku gan ƴan wasa kaman Ibrahim Madawari, Sadiq Sani Sadiq, Akawu, Hauwa Maina, Shehu Hassan Kano da kuma Fati Shuʼuma.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

kasa-ta

 

7. Ƙasa ta

Wannan wasa yana gabatar da Ali Nuhu, Rahama Sadau, Sadiq, Hauwa Maina da Hadiza Muhammad. Wannan wasa “Ƙasa Ta”, wasa ne akan Siyasa. Auwal shi ne darektan.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

mahaukaciya

 

8. Mahaukaciya

A cikin wannan wasa, Jamila Umar Nagudu ita ce a matsayin jagorancin wasan “Mahaukaciya”. Zaɓen ʼƳan wasan wannan shiri su ne: Sulaiman Bosho, Aminu Daggash, da Haruna Kutama.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

maula

 

9. Maula

Wannan wasa ne mai ban tausayi. Ali Gumzak shi ne darektan wasa.

A danna nan domin kallon gabatarwan shiri.

nabisi

 

10. Nasibi

Ƴan wasan kwaikwayon Kannywood wanda sun fita cikin wannan wasa su ne: Ali Nuhu tare da Maryam Gidado. Abubakar Shehu shi ne darektan wasa.

You may also like