Kano, Nigeria —
Allah ya yi wa shahararren Daraktan bangaren fina finai na shiyyar Kano ko kannywood, Aminu Surajo Bono, rasuwa da yammacin yau Litini.
Shahararren Daraktan, wanda kuma tsohon gogaggen jarumi ne, ya rasu ne cikin gajartaccen lokaci bayan lalurar, a cewar majiyoyi.