Fitaccen wasan kwaikwayon talabjin na Somalia da ya fito da matsalolin haramtattun abubuwan da ke faruwa



G

Asalin hoton, ABDISHUKRI HEYBE

Bayanan hoto,

Yanzu Novice Shukri Abdikadir na son cimma burin zama ‘yar wasan kwaikwayo bayan da ta fito a a tauraruwar fim din Arday

Shin wa zai naɗi wasan kwaikayo mai dogon zango na Talabijin mai kashi 10 a birnin da ya fuskanci rikicin shekaru 30, da matasan da ba su taɓa shiga fim ko wasan kwaikwayo ba?

Amsar ita ce Ahmed Farah.

Shi ne daraktan wasan kwaikwayo na Arday ko “Ɗalibi”, wanda aka naɗa a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, kana aka kaddamar a ranar Alhamis a tashar talabijin na Bile na kasar.

Ya yi fito-na-fito da wasu daga cikin abubuwa mafi cike da ce-ce-ku-ce a ƙasar, da suka haɗa da fina-finan batsa, da fyade, da miyagun kwayoyi da kuma ‘yan daba ‘yanmata – duka haramtattun abubuwa a kasar ta Somalia.



Source link


Like it? Share with your friends!

3

You may also like