Fitacciyar Jarumar Finafinan Amurka, Lindsay Lohan Ta Musulunta Rahotanni sun nuna cewa fitacciyar jarumar finafinan kasar Amurka, Lindsay Lohan ta karbi Musulunci.
Jarumar ta sanar da hakan ne a shafinta na Instagram, inda ta goge dukkan tsoffin hotunanta tare da sanya sabbi wadanda suke da alaka shigar Musulunci tare da rubuta kalmar ‘salamu alaikum.
Idan za a iya tunawa an yi ta kalubalantar jarumar a shekarun baya a kasar Amurka a lokacin da ta yabi musulunci sannan aka ganta dauke da Kur’ani.

You may also like