Fitacciyar ‘Yar Fim Rashida Adamu Ta Zama. Shugabar Mata Matasan Jam’iyyar APC Na Arewa. 



Fitacciyar jarumar finafinan Hausan nan, kuma mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin mata, wato Rashida Adamu wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a ta zama shugabar mata na kungiyar matasan jam’iyyar APC na yankin Arewa mai dauke da jihohi sha tara.
Taron wanda aka gudanar a garin Kaduna, jarumar ta yi nasarar samun matsayin ne bayan ta kada abokan takararta mata guda takwas.
A yayin jin ta bakin Hajiya Rashida game da wannann shugabanci da ta samu, ta bayyanawa manema Labarai cewa ta yi matukar farin ciki da zaben nata da aka yi, sannan kuma bayan ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi fatan Allah ya taya ta rikon wannan matsayi.
Baya ga wadannan mukamai, Rashida ita ce shugabar mata ta kungiyar Social Media ta jihar Kano, sannan kuma Jakadiyar Arewacin Nijeriya ta masu shirya finafinai.

You may also like