FITAR ATIKU DAGA APC BA WANI MATSALA BANE – CEWAR GWAMNA OKOROCHA Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi ikirarin cewa matakin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya dauka na ficewa daga APC babbar matsala ce ga jam’iyyar inda ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin gogaggen dan siyasa.

Sai dai Gwamnan wanda shi ne Shugaban kungiyar gwamnonin APC, ya jaddada cewa gwamnonin jam’iyyar sun rigaya sun tsayar da Shugaba Buhari a matsayin dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019 wanda hakan ya saba ra’ayin tsohon Gwaman Legas kuma jigo a jam’iyyar, Bola Tinubu wanda ya jaddada cewa jam’iyyar ba ta tsayar da kowa dan Takararta ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like