Fitar Da Daliban Kano Kasashen Ketare Don Yin Digirin Farko Ko Na Biyu Na Gwamnatin Kwankwaso Zamba Ne-Ganduje


Kano-State-...Governor-Abdullahi-Umar-Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce shirin bayar da tallafin karo karatu a kasashen ketare da tsohuwar Gwamnatin jihar tayi duk zamba ne.

 

Yace a madadin abi ka’ida wajen biyan kudaden daliban sai Gwamnatin baya ta hada baki da wasu yan kwangila, su ake turawa kudaden daliban, su zari kasonsu sannan su mikawa daliban ragowa, hakazalika idan batun biyan kudin makaranta ya tashi, yan kwangilar ake turamawa su zari rabonsu sannan su je su biya.

 

Ganduje ya yi wannan zargi ne a lokacinda ya karbi bakuncin sabbin shugabannin kungiyar dalibai yan asalin jihar Kano, NAKSS, wadanda suka ziyarceshi.

 

Ya ce Gwamnatinsa ba zata lamunci wannan abun takaici da rashin gaskiya da zalinci ba.

 

Ganduje ya kuma sha alwashin cigaba da biyawa daliban kudaden tallafin karatun har su kammala karatunsu.

 

Ya ce Gwamnatinsa ta yi kokarin biyan tulin bashin da ta tarar makarantu da Daliban na bin jihar wanda har yanzu akwai ragowar kusan Naira Biliyan N3 da ake bin jihar bashi.

 

Ya kuma ce hatta a makarantun cikin gida akwai bashin fiye da Naira Biliyan N2 da jami’oi ke bin tsohuwar Gwamnati, baya ga haka kuma Gwamnatin bata biya daliban ba har tsawon shekara Hudu.

 

Hakama aikin jami’ar Arewa maso Yamma inji Gaduje aikin ya tsaya cak kimanin shekara Biyu, har sai zuwan Gwamnatinas a inda ta bukaci ma’aikatan su cigaba da aiki.

 

A saboda haka sai Gwamnan ya shawarci daliban da su kaucewa yan hauma-hauma wadanda basu da aiki sai yiwa Gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa.

 

A nashi jawabin shugaban daliban, NAKSS, Aliyu Muhammad Maikasuwa Rano, ya shaidawa Gwamnan cewa dukkanin mambobinsu 57 suna goyon bayanshi a yunkurin bayar da ilimi bai daya a kyauta.

 

A cikin sanarwar da Daraktan yada labarai na fadar Gwamnatin jihar, Salihu Tanko Yakasai ya fitar,

 

Ya ce Gwamnan ya kuma bawa kungiyar matasan Nigeria kyautar falleliyar mota wacce, Kabiru Ado Lakwaya, ya karba a madadinsu.

 

Lakwaya ya kuma godewa Gwamnan sosai bisa wannan gudunmuwa.

You may also like