
Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon tawagar Netherlands Frenkie de Jong na jinya a Barcelona, wanda bai buga wa kasarsa wasa da Faransa ba.
Ranar Juma’a Faransa ta ci Netherlands 4-0 a wasan farko a cikin rukuni a neman shiga Euro 2024 da za a yi a Jamus.
Tun farko an gayyace shi wasan, amma raunin da ya ji ya hana shi zuwa buga fafatawar ta hamayya.
Daga wasa bakwai baya da Netherlands ta buga da Faransa, an doke ta shida daga ciki, inda Kylian Mbappe ya fara aikin kyaftin, bayan da ya maye gurbin Hugo Lloris, wanda ya yi ritaya.
Bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Qatar da Faransa ta yi ta biyu, Karim Benzema da Raphael Varane suka sanar da yin ritaya.
Barcelona ba ta fayyace girman raunin da De Jong ya ji ba, balle a tantance ranar da zai warke ya koma buga mata tamaula.
De Jong ya buga wa Barcelona wasa 34 a bana da cin kwallo biyu ya bayar da daya aka zura a raga.
‘Yan kwallon Barcelona da ke gaban De Jong a yawan yi mata tamaula a kakar nan sun hada da Ter Stegen da Lewandowski da kuma Gavi.
Ranar Asabar Barcelona za ta ziyarci Elche a wasan La Liga.
Shi kuwa sabon kocin Netherlands, Ronald Koeman wanda ke aiki a tawagar karo na biyu zai fafata da Finland ranar 26 ga watan Maris a gida.