
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong mai shekara 25 ya shaida wa kocin Manchester United Erik ten Hag cewa zai ji daɗi idan ya koma Old Trafford. (Mirror)
West Ham ma na son ɗaukar ɗan wasan Manchester United da Ingila Aaron Wan-Bissaka mai shekara 24 a matsayin aro a watan Janairu bayan an buɗe cinikin ƴan wasa. (Manchester Evening News)
Ɗan wasan tsakiyar Fiorentina da Morocco Sofyan Amrabat mai shekara 26 zai zaɓi ya koma Liverpool duk da cewa kulob din hamayyar Liverpool ɗin a Firemiya wato Tottenham na harin ɗan wasan. (Foot Mercato via Inside Futbol)
Ana kyautata zaton Amrabat ɗin zai iya komawa Liverpool a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan motsawar ɗan wasan Borussia Dotmund da Ingila Jude Bellingham mai shekara 19 da kuma ɗan wasan Benfica da Argentina Enzo Fernandez mai shekara 21. (Team Talk)
Chelsea da Liverpool na son ɗaukar ɗan wasan Brighton da Ecuador mai shekara 21 Moises Caicedo. (Sky Sports)
Barcelona na son sayen ɗan wasan gaban Jamus mai shekara 18 Youssoufa Moukoko daga Borussia Dortmund amma sun ƙi biyan kuɗin tafiyar wani ɗan wasa a kyauta a watan Yuni. (Football Transfers)
Chelsea na son ta samu nasara kan Real Madrid da Manchester City wurin sayen ɗan wasan RB Leipzig da Croatia Josko Gvardiol mai shekara 20 ta hanyar nuna cewa za ta biya fam miliyan 45 a kansa a watan Janairu. (Sun)
Rahotanni na cewa Manchester United na neman sayen dan wasan Borussia Monchengladbach da Faransa Marcus Thuram mai shekara 25 a watan Janairu. (Sport Bild via Sun)
Kocin Atletico Madrid Diego Simeone na farautar ƴan wasan baya inda cikin waɗanda yake hari har da ɗan wasan bayan Leicester City da Turkiyya Caglar Soyuncu mai shekara 26. (Team Talk)
Kocin PSV Eindhoven wato Ruud van Nistelrooy ya bayyana cewa ba shi da damar hana ɗan wasan Netherlands mai shekara 23 Cody Gakpo barin kulob ɗin. (90min)