Fulani Makiyaya Ba Yan Ta’adda Bane A cewar Garba Shehu 


Kakakin Shugaban kasa Garba Shehu yace Fulani masu kashe mutane ba yan ta’adda bane face wasu gungun mutane bata gari.

Shehu, ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da gidan talabijin na Channels a yau Alhamis. Yace gwamnatin bata aiyana Fulani da suke kashe mutane  a matsayin yan ta’adda ba  saboda su kawai wasu gungun mutane ne bata gari. 

Amma yace jami’an tsaro suna maganin Fulanin kamar yadda doka ta tanada. 

“Akwai banbanci tsakanin aiyukan ta’addanci da kuma na aiyukan bata gari, wasu daga cikin Fulani bata garine  kuma ana yin maganinsu kamar yadda doka ta tanada,” yace. 

“Amma IPOB kamar kungiyar Boko Haram sun ware wani bangare da suke kira nasu, a matsayin kasa mai cin gashin kai kuma sun nuna kokarin mamaye wasu makotan jihohi. Sun saka damuwa a jihohin Kogi da Benue. Sun kuma ce suna son karbar jihohin Bayelsa da Rivers irin wannan ne abinda kungiyar Boko Haram tayi. Dokar kasa  baza ta taba amincewa da haka ba,”yace. 

Ranar Juma’ar da ta gabata ne rundunar sojin Najeriya ta aiyana kungiyar ta IPOB a matsayin kungiyar yan ta’adda  yayin da gwamnonin yankin kudu maso gabas suka haramta kungiyar.

A ranar Laraba kuma wata kotun tarayya dake Abuja ta bada umarnin saka kungiyar ta IPOB cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda. 

You may also like