Fulani makiyaya sun lalata coci sama da 500 a  Benue


Akpen Leva, shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Benue ya ce fulani makiyaya sun lalata ginin coci sama da 500 a jihar.

Da yake magana da yan jaridu a Makurdi ranar Talata, Leva ya bayyana barnar da aka yi a matsayin “abin damuwa” inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan tabiya diya ga cocin da abin ya shafa.

Shugaban ya ce yawancin wadanda rikicin ya shafa Kiristoci ne hakan ya sa majami’u dake jihar su ke kula da kusan mutane 170,000.

“Barnar ta shafi kiristoci mabiya darikar Katolika, Pentacostal, NKST, Anglican da sauran coci da dama dake yankunan da rikicin ya shafa,” ya ce.

Jihar Benue dai ta fuskanci hare-hare daga wasu mutane da ake kyautata zaton fulani makiyaya ne.

You may also like