Fulani Sun Kai Hari Kan Wani Masallaci,Inda Suka Kashe Liman Da Kuma Mutane 20 A jihar Neja


Wasu yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sunkai hari kan wani masallaci na al’ummar garin Etogi, dake karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja. 

Harin yafaru ne lokacin da mutanen garin suke gudanar da sallar asuba.

Wasu mata da yara suma sun samu rauni a harin.

A cewar majiyar jaridar The Nation, harin na ramuwar gayya ne, biyo bayan fadan da akayi tsakanin Fulani da al’ummar garin.

A cewar jaridar sabanin ya biyo bayan kin biyan cikon kudin gona  da al’ummar garin suka bawa Fulanin. 

Fulanin sun dage cewa gonar tasu ce. 

Rundunar yan sandar jihar Neja ta tabbatar da faruwar harin inda yace ” harin na ramuwar gayya ne kan bafulatanin da aka kashe sakamakon sabani tsakanin Fulani da al’ummar garin. ”

Bala elkanah mai magana da yawun rundunar yan sandar jihar yace mutane 20 ne suka rasa rayukansu.

Yace mutane takwas da suka samu rauni a harin na can na karbar magani a asibiti.

Elkanah yace tuni zaman lafiya  ya dawo garin.

Sai dai wasu mazauna garin sunce har yanzu suna cikin zaman dar-dar inda suka nemi da a kara tura jami’an tsaro zuwa yankin. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like