Fursunoni 4 aka harbe 36 suka tsere daga gidan yarin Akwa Ibom


Fursunoni 8 aka harbe har lahira ranar Laraba lokacin da suke ƙoƙarin guduwa daga gidan yarin Ikot Ekpene dake jihar Akwa Ibom.Wasu kuma 36 suka tsere daga gidan yarin.

Ogbajie Ogbajie,mai magana da yawun hukumar dake kula da gidajen yari ta Najeriya a jihar Akwa Ibom ya ce tunda fari fursunonin sun kai hari kan masu aiki a wurin  dafa abinci kafin su tsere ta kofar dake bayan gidan yarin.

” Da misalin karfe 11:45 na ranar Laraba, 27 ga watan Disamba an samu afkuwar kai hari kan ma’aikatan dake bakin aiki a wurin dafa abinci na gidan yarin Ikot Ekpene daga wasu daurarru dake gidan yarin,”Ogbajie ya bayyana haka a cikin sanarwar.

“Sun kwace gatari a hannun wani fursuna dake aiki a wurin dafa abincin suka kuma yi masa mummunan sara a ka daga nana kuma suka doshi kofar dake bayan gidan yarin sun yi amfani da gatarin wajen ɓalle kofar daga nan kuma suka shiga faɗa da jami’an tsaron da suka yi kokarin kamo su.

“A karshe huɗu daga cikinsu da suka samu harbin bindiga sun rasa rayukansu  yayin da aka sake kama 7 wasu 36 kuma suka tsere tuni aka tura jami’an tsaro domin su nemo su.”

Alex Odita, kwantirolan gidajen yari na Akwa ya bada umarnin ayi bincike kan lamarin.

You may also like