Fursunoni sun tayar da hayaniya a wani gidan yarin Faransa


 

 

A yammacin Litinin din nan wasu fursunoni sun tayar da hayaniya a gidan yarin Vienne da ke kusa da garin Poitiers na kasar Faransa inda suka kashe gandiroba 1.

Fursunonin sun fara hayaniyar ne bayan sun kwace mukullin kofar shiga inda suke.

Mutanen sun kuma tayar da gobara a gidan kurkukun.

An samu nasarar kwantar da rikicin bayan anaike da jami’ai na musamman.

Ma’aikatan kashe gobara sun samu nasarar kashe wutar da ta kama.

Babu wani fursuna da ya jikkata ko mutu amma kuma wani gandiroba ya shake da hayaki.

Jami’an ytsaro sun kama shugaban wadanda suka faro rikicin.

Akwai fursunoni 219 a gidan yarin na Vienne.

You may also like