An gabatar da kudirin hana saka cikekken Hijabi a kasar Jamus


 

Gwamnatin kasar Jamus ta amince da wata doka da aka gabatar mata na hana saka cikekken hijabi da kuma Nikabi a wasu wuraren kasar

Kamfanin dillancin Labaran Tasnim ya nakalto thomas de Maiziere Ministan cikin gida na kasar Jamus a wannan Alkhamis na cewa Gwamnati ta amince da wani kudiri da aka gabatar mata na hana saka cikekken hijabi daga ciki har da saka nikabi.

A watanin da suka gabata ne Gwamnatin ta Jamus ta bijuro da maganar hana saka Burka’i watau Hijabin dake rufe dukkanin jiki har da fuska a wasu wurare na kasa. ana sa ran za a fitar da wata sabuwar doka a kasar ta Jamus wacce za ta tilastawa masa musulmi hana rufe fuskokin su a kasar.

Wannan doka dai Ma’aikatar cikin gidan kasar ce ta gabatar da ita, kuma ta samu amincewar dukkanin manbobin Majalisar zartarwar na kasar Jamus, dan haka ana sa ran nan da ‘yan kwanaki za a haramtawa Mata musulmi rufe fuskokinsu a cikin kasar.

You may also like