Gabon: Ali Bongo ya fara wa’adi na biyu.


A kasar Gabon an rantsar da Ali Bongo don fara shugabancin kasar a wa’adi na biyu.

35881901_303

 

Ranzar da shugaban kasar ta Gabon dai ya biyo bayan hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ya yanke,inda ya amince da nasarar Ali Bongo. Wani mazaunin Libreville babban birnin kasar ta Gabon, ya fadawa manema labarai cewa, su kam rayuwarsu ta dame su bawai harkar ‘yan siyasa ba. Domin  abin da suke yi walau ta bangaren gwamnati ko ‘yan adawa ba komai bane, illah son kansu kawai. “Duk abinda suka yi don kansu ne, mu kuma duk abinda muke yi shi ne, mu jira kura ta lafa a kasar. Muna da iyalai, muna da ‘yan uwa, muna da yara, kuma dukansu muna so su je makaranta. A gefe guda su kuma ‘yan siyasa ya kamata su fita harkar kasa su yi nasu sha’anin”

You may also like