
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier League da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City ta biyu.
Gunners ta doke Leeds United 4-1 a wasan mako na 29 a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka kara ranar Asabar a Emirates.
Gabriel Jesus ne ya ci biyu daga ciki, karon farko da ya ci wa Arsenal kwallo tun cikin Oktoba a wasan da Gunners ta ci Tottenham 3-1 a Premier League.
Dan wasan tawagar Brazil ya ci wa Gunners kwallo biyar a wasa takwas da ya fara yi tun bayan da ya koma Emirates daga Manchester City a Yulin bara.
Tun daga nan bai sake cin kwallo a Arsenal ba a dukkan fafatawa har sai wasan hamayya da Tottenham a Lik.
Ranar Asabar aka fara wasa da Jesus a Arsenal a tamaula, bayan da ya sha jinya sakamakon raunin da ya ji a gasar kofin duniya a tawagar Brazil a Qatar a 2022.
To sai dai ya shiga canji a karawar da Gunners ta casa Crystal Palace 4-1 a wasan Premier League ranar 19 ga watan Maris.
Tun kan nan ya fuskanci Fulham a League Cup, wanda ya yi minti 13, ya buga wasa da Sporting minti 45, sannan da Crystal Palace.
Gabriel Jesus ya zura kwallo 52 a raga a Premier League a City da Arsenal, daga ciki aka yi nasara 49 da canjaras uku a ranar da ya ci kwallayen.
Gabriel Jesus ya buga kwallo zuwa raga sau 42 a wasa 17 a Premier League a kakar nan, yayin da 23 daga ciki suka nufi raga kai tsaye.
Arsenal wadda ke fatan lashe Premier League a bana a karon farko tun bayan 2003/04 ta bai wa City tazarar maki takwas, saura wasa tara a kare kakar nan.