An sake dage shari’ar da ake yi wa tsohon mai ba wa shugaban kasar Nijeriya shawarar kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki (rtd) tare da wasu mukarrabansa bisa zargin sama da fadi kan kudaden sayen makamai da aka waye har zuwa ranar 25 ga watan Janairu na shekara mai kamawa saboda rashin lafiyar daya daga cikin wadanda ake zargin.
Rahotanni sun ce alkalin kotun mai shari’a Baba Yusuf ya sanar da dage shari’ar ne bayan ‘yan gajeruwar zaman da aka yi a kotun saboda rashin halartar mutum na biyu da ake zargi a shari’ar Salisu Shu’aibu wanda lauyarsa ya ce an kwantar da shi ne a asibiti saboda rashin lafiyar da yake fama da shi, shi ne dalilinsa na rashin halartar kotun.
Alkalin kotun ya ce bisa la’akari da cewa wannan shi ne karon farko da wanda ake zargin bai sami damar halartar kotun ba don haka ya dage sauraren karar har sai zuwa ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 2017 mai kamawa wanda ake fatan kafin lokacin ya sami sauki.
Hukumar fada da ta’annuti ga tattalin arzikin Nijeriyan EFCC ne dai ta gurfana da Kanar Dasuki tare da Salisu Shu’aibu tsohon daraktan kudi a ofishin babban mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron da kuma wasu mutane na daban bisa zargin sama da fadi kan wasu kudade sama da Dala Biliyan 2.1 da aka ware don sayen makamai na fada da kungiyar nan ta Boko Haram.