Zababben shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ya nufi kasar Mali tare da tawagar shiga tsakani ta kungiyar ECOWAS inda zasu halarci taron Faransa da kasashen Afrika.
Kamar yadda ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaidawa manema labarai a kasar ta Gmabia ya ce tawagar ta ECOWAS ta dauki matakin tafiya da Adama Barrow a taron, bayan tattaunawa da shugaba Yahya Jammeh da zabbaben shugaban kasar a Jiya Juma’a.
Shugabannin kasashen kungiyar dake shiga tsakani sun dai isa birnin Banjul ne da nufin lallashin Jammeh ya mikawa Barrow mulki cikin ruwan sanyi a ranar 19 ga watan Janairu nan.
Saidai bayanai daga kasar sun ce da alamu dai tattaunawar bata haifar da wani sabon abu ba, inda yanzu tawagar da shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ke jagoranta ta nufi birnin Bamako na kasar Mali domin ganawa da sauran shugabanin kasahen mambobin kungiyar ta Ecowas domin tattauna matakin da zasu dauka.
Kasar Gambia ta shiga halin rashin tabbas ne tun lokacin da shugaban kasar mai barin gado Yahya Jammeh ya ce bai yarda da sakamakon zaben shugaban kasar ba da aka gudanar a farkon watan Disamba bara, bayan da farko ya amince da shan kaye a zaben.
kafin nan dai Jammeh ya ce ba zai sauka daga mulki ba, har sai kotun kolin kasar ta yanke hukuncin akan karar da ya shigar wanda ake sa ran kotun zatayi a watan Mayu mai zuwa.