
Asalin hoton, WHO
Hukumar lafiya ta duniya ta gshawarci mahukunta da su dai na siyar d maganin tarin guda hudu da aka samar da su a India
Wani kwamitin majalisar dokokin Gambiya ya bukaci a hukunta kamfanin samar da maganin tari na kasar Indiya da ake zargin ya yi sanadiyar mutuwar kusan yara 70 a kasar.
Kwamitin ya ce laifin kamfanin Maiden Pharmaceticals ne da ya shigo da maganain da yake gurbatace, zuwa kasar don haka dole ya amince da aikata ba daidai ba.
Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargaadi a watan Octoban da ya gabata, inda ta shawarci mahukunta da su dakatar da sayar da maganin tarin.
Sai dai kamfanin Maiden Pharmaceutical ya musanta zargin.
Dakin gwaje-gwaje kimiyya na gwamnatin India, da ya gudanar da binciken maganin tarin, ya gano cewa suna an “suna bin ƙa’idar da aka gindaya wajen samar da maganin”.
A makon da ya gabata wani jami’in kasar Indiya, ya ce hukumar lafiyar ta duniya “ta gina zargin ta kan zato” wajen zargar maganin tarin.
Bayan makoni da suka dauka suna na bin cike, kwamitin majalisar Gambiya, ya shawarci mahukunta kasar da su dauki matakai masu tsauri, ciki har da haramata siyar da kayan kamfanin Maiden Pharmacetucal a kasar baki daya, kuma su dauki matakin shari’a kan kamfanin.
Kwamitin ya ce ya gamsu cewar kamfanin Maiden Pharmacetucals na da laifi kuma ya kamata a tuhume shi da laifin shigo da maganin mara kyau.
“Sakamakon rahoton da ya zo daya da wanda aka samar a baya, ya nuna cewar magungunan tari na yara na Promethazine Oral solution, da Kofexmalin, da Makeoff, da Magrip, dukkan sun gurbace da sinadarin diethylene glycol, da ethylene glycol,” a cewar rahoton kwamitin majalisar.
Diethylene glycol and ethylene glycol, na da illa ga dan adam, da za su iya halaka mutum idan ya sha.
Sai dai kwamitin ya ce har yanzu ana ci gaba da bin ciken kimiya don gano ainihin musabbabin mutuwar yaran.
Kwamitin kuma na son hukumar da ke kula da maguguna ta Gambiya da ta tabbar da an yi rajistar dukkan magungunan da aka shigo da su kasar, da kuma yin bincike kan kamfanin da ke samar da shi, har da ziyartar inda suke hada maganin.
Rahoton kuma ya gano matsaloli bangaren lafiyar kasar ke fuskanta, inda suka bukaci gwamnati da ta karfafa tare da samar da ingantatun kayan aiki da magunguna a asibitocin ƙasar.
Me ya faru?
A ƙarshen watan Yulin da ya gabata ne Gambiya ta gano yadda ake samun karuwar yarad ba su kai shekara biyar da ke fama da matsalar ƙoda.
Daga bisani gwamnatin kasar ta ce kimanin yara 69 sun mutu sakamakon wannan matsalar.
Majalisar dinkin duniya ta WHO ta gano magunguna kamfanin Maiden Pharmaceuticals 4 da alaƙa mai ƙarfi, da mace-macen yaran na Gambiya, wadan hakan ya sa suka bayar da gargadi ga sauran kasashen duniya.
Bayan da labarin ya bulla a watan Octoba, India ta ce tana bincike kan magungunan, sannan suka umarci kamfanin Maiden Pharmaceuticals da ya dakatar da hada maganin a babban kamfanin su da ke arewacin jihar Haryana.
A ranar 13 ga Disamba, shugaban kula da shige da ficen magunguna a Indiya Dr. VG Somana wata takarda da ya rubutaw WHO, ya ce samfuran magunguna da gwamnati ta yiwa gwajin kimiya, ba su lalace ba, da sinadaran da ake fada ba.
“Dangane da binciken kimiya da muka samu daga dakin wagje-gwaje na gwamnati, dukkan samfuran magungunan 4 da mu ka auna, ya nuna cewar suna bin ƙa’idoji da samar da magani, a cewar sa.
Wani kwamitin ƙwararru na India na faɗaɗa bincike kan sakamakon gwajin na kimiyyar.
A makon da ya gabata wani babban mai bayar da shawara ga ministan yaɗa labaran India, ya faɗa wa BBC cewar a gadarance hukumar WHO ta dora wa laifin mutuwar yaran ga maganin tarin.
“Duk binciken da nazarin da kwararu ma’aikatan gwamnatin Indiya suka yi, ya nuna cewar kalaman gadar da hukumar WHO ta yi babu ƙanshin gaskiya a cikinsa, ba kuma daidai ba ne,” a cewar Kanchan Gupta.
Haka kuma lafiyar na da makami ba tare da wata ƙwaƙwaran dalili.
Indiya ce ƙasa ta uku a duniyar wajen samar da magani, kuma mafi akasarin su maganin kwaya ne.
Hakan ya sa ta zama gida ga kamfanin hada magunguna masu yawa da ke tasowa cikin ƙanƙanin lokaci, da ake kira “Duniyar haɗa magani” kuma suke samar da mafi akasarin magungunan da ake buƙata a ƙasashen masu yawa a Afirka.