Ganawa tsakanin Merkel da May


Screen Shot 2016-07-19 at 1.28.59 AM

Firaministar Birtaniya Theresa May na shirin kai wata ziyara zuwa Berlin babban birnin Tarayyar Jamus, a karo na farko na ziyararta zuwa kasashen ketare tun bayan da ta dare kan karagar mulki.

Firaministar Birtaniya Theresa May da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

A ranara Larabar makon da ya gabata 13 ga wannan wata na Yuli ne dai May ta karbi ragamar mulki daga hannun tsohon Firaministan Birtaniyan David Cameron. A yayin ziyarar tata Firaminista May za ta gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da yammacin ranar Laraba 20 ga wannan wata na Yuli da muke ciki, inda za su tattauna batutuwa da dama da suka hadar da halin da ake ciki bayan yunkurin yin juyin mulki a Turkiya da batun ‘yan gudun hijira da kuma na ficewar Birtaniyan daga EU. Bayan sun kammala tattaunawar da kuma gudanar da taron manema labarai, an shirya cewa May da Merkel za su ci abincin dare tare.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like