Muhammad Jawad Zarif Ya gana da takwaransa na Cote De Voire Abdullah Mabry, a nan Tehran a yau lahadi
Muhammad Jawad Zarif Ya gana da takwaransa na Cote De Voire Abdullah Mabry, a nan Tehran a yau lahadi.
Majiyar diplomasiyya anan Tehran ta sanar da cewa; Ministocin biyu sun yi ganawar ne a nan Tehran, inda su ka tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen su.
Ministan harkokin wajen kasar ta Cote De Voire Abdullah Mabry, ya yi ishara da taron kwamitin hadin guiwa na kasashen biyu wanda aka yi a shekarar 2017 a birnin Abidjan, sannan ya jinjinawa jamhuriyar musulunci ta Iran akan rawar da ta ke takawa ta fuskar siyasa da tattalin arziki.
Bugu da kari, Mabry ya kara da cewa; Kasashen biyu kuma za su iya aiki tare a fagagen ilimi da bankuna da aikin gona da kare hakkin bil’adama da fada da ta’addanci da muggan kwayoyi.