Ganduje Da Shugaban Jam’iyya Sun Garzaya Abuja Domin Dakatar Da Kwankwaso Zuwa Kano


Wata kwakkwarar majiya daga jam’iyyar APC ta jihar Kano ta shaidawa Arewa24news cewa, Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da rakiyar shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano Injiya Bashir Karaye sun garzaya birnin tarayya Abuja domin kulle-kullen dakatar da ziyarar Sanatan Kano ta tsakiya Rabi’u Musa Kwankwaso da ya shirya kawo jihar Kano ranar 30-1-2018.

“Jiya bayan kammala taron Bichi muka raka shi filin jirgi suka tafi Abuja kusan misalin karfe 10:00 na dare”. Inji majiyar.

You may also like