Ganduje Ya Bada Umarnin Cire Duk Wani Abu Mai Launin Ja Dake Dakin Taro Na ‘Coronation Hall ‘ Gwamnatin jihar Kano ta sauya launin dakin taro na Coronation Hall dake gidan gwamnatin jihar daga launin ja zuwa Kore.

Tsohon Gwamnan jihar  Rabiu Musa Kwankwaso ne ya gina dakin taron, a shekarar 2015 domin gudanar da bikin mikawa sarkin Kano Muhammad sunusi II sanda. 

Dakin taron dai anyi masa adon launin Ja dake nuni da kalar darikar kwankwasiyya ta tsohon gwamnan.

Gwamna Ganduje, ya dade yana takun saka da tsohon gwamnan, har takai magoya bayansa sunyi watsi da saka  jar hula alamun dake nuna sun raba gari da darikar ta kwankwasiyya.

Sai dai mai magana da yawun gwamnan Salihu Tanko yakasai yace an sauya kujerun dakin taron ne Saboda wasunsu sun fara lalacewa.

Ya kuma kara da cewa an sauya launin dakin taron  ne daga kalar ja zuwa Kore domin ya saje da yadda kalar saura gine-gine na gidan gwamnatin suke

You may also like