Ganduje Ya Kafa Harsashin Katafaren Kasuwar ‘Yan Tebura Mall


 

 

 

 

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kafa harsashen ginin katafaren sababbin shaguna da aka yi wa lakabi da ” ‘Yan Tebura Mall” da kuma shaguna da tituna guda tara da ake yi a sauran sassan kasuwar Kantin Kwari.

 

A jawabin sa, Gwamna Ganduje ya fada wa al’ummar kasuwar Kwari da na jihar Kano baki daya cewa, wannan katafaren aiki na zamanantar da kasuwar Kwari, daya ne daga cikin ayyukan zamanantar da kasuwanni guda hudu da za a inganta matsayinsu don habbaka harkar kasuwanci a jihar.

 

 

 

Sauran su ne kasuwar Rimi, da ta Kofar Wambai, da kuma Dawanau. Gwamna Ganduje ya kara da cewa bayan kammala wannan aikin na Kwari za a samar da shaguna kusan dubu daya sannan za a gina sababbin gini guda biyu masu suna ‘YAN TEBURA MALL da za a samarwa da ‘yan tebura guda dubu hudu da dari daya da sha shida matsuguni ingantatce.

 

Shima Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II ya yabawa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR bisa wannan aikin wanda ya ce tun a lokacin da aka fara shirye-shiryen aiwatar da aikin ya bada goyon bayan sa saboda kimar aikin da yadda zai inganta kasuwanci a jihar. Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bawa gwamnati goyon baya don ci gaba da ayyukan alheri.

 

 

yan-tebura6-760x570

 

Taron ya samu halartar wakilin kakakin majalisar jihar Kano, da Kwamishinoni, da manyan jami’an gwamnati, da Kwamishinan ‘yan sanda na jihar da sauran manyan ‘yan kasuwa da attajirai.

 

 

yan-tebura3-760x570 yan-tebura7-566x377 yan-tebura5-760x570 yan-tebura6-760x570 yan-tebura2-760x570

You may also like