Ganduje ya lalata miyagun ƙwayoyi na biliyan ₦1


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ranar Juma’a ya lalata miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira biliyan ₦1 da aka kwace a wurare daban-daban dake faɗin jihar.

Ganduje ya bayyana cewa wannan wata babbar nasara ce da aka samu a yaƙin da gwamnatinsa take yi kan sayarwa da kuma shan miyagun ƙwayoyi.

Gwamnan yace gwamnatin jihar a kwanannan ta sake faɗaɗa cibiyar warkar da masu shan miyagun ƙwayoyi dake jihar.

Ya shawarci ɗai-ɗaikun mutane da kuma ƙungiyoyi kan su taimakawa yunƙurin gwamnati na yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi domin samar da al’umma tagari.

Ganduje ya kuma yi kira kan a rika  gaggauta yi wa masu sayarwa da safarar miyagun kwayoyi a tare da yanke musu hukuncin zaman gidan yari mai tsawo.

You may also like