A yayin da wasu gwamnoni ke kokarin aiwatar da dokokin hana kiwo a jihohinsu, Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya nemi dukkanin Fulani makiyaya da ke kasar nan musamman na jihohin Taraba da Binuwai kan su koma jiharsa.
Gwamnan ya ce Kano na da isasshen filayen kiwo da Fulani makiyayan za su aje dabbobinsu inda ya ce a halin yanzu gwamnatin jihar tana rajistar makiyaya da dabbobinsu a wani mataki na kula da su da kuma dabbobinsu. A halin yanzu dai, an fara yi wa Shanu sama da milyan daya allurar rigakafi a jihar.