Majalisar Dokokin Jihar Kano  Ta Dakatar Da Binciken Da Take Yiwa Sarki Sunusi 


Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da binciken da take yiwa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, 

Majalisar ta dau wannan mataki ne bayan da shugabanta Kabiru Alhasan Rurum ya karanta wata takarda da gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya rubutowa majalisar.

A cikin takardar da ya aikewa majalisar Ganduje ya lissafa wasu mashahuren mutane da suka hada da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo,Aminu Dantata, Abdussalam Abubakar,Ibrahim Babangida, Sarkin Musulmi Saad Abubakar da kuma Aliko Dangote da sauransu a matsayin wadanda suka  rokeshi da yayafewa sarkin. 

Da yake rokon yan majalisar kan su dakatar da binciken, gwamnan yace sakamakon zaman sulhun da sukayi a Kaduna, Sarkin ya amince da dukkanin kurakurensa kana ya bada hakuri. 

Wani dan majalisar da yanemi a sakaya sunansa yace gwamnan ya nemi su dakatar da binciken saboda girman mutanen da suka saka baki a maganar bawai dan sarkin bashi da laifi ba. 

Tuni majalisar ta amince da rokon da gwamnan yayi da gagarumin rinjaye. 

You may also like