Ganduje Ya Taya Kwankwaso MurnaWata majiya daga jihar Kano ta tabbatar da cewa, Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon maigidan sa, kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cikarsa shekaru 61 a duniya.
Ganduje ya aika da wannan sako ne ta kafafen yada labarai, inda a ciki ya yi masa fatan alheri da karin albarka a rayuwarsa tare da fatan rayuwarsa ta zama alheri ga al’ummar jihar Kano baki daya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da kiraye kirayen samun hadin kai da zaman lafiya a tsakanin shugabannin biyu, wadanda ake ganin hadin kan nasu zai haifarwa jihar babban alheri. 

You may also like