Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tabbatar da nadin Mustafa Hamza Buhari a matsayin mai bada Shawara kan Harkokin Siyasa.
Wannan jawabi ya futo ne daga Salihu Tanko Yakasai shugaban yada labari na jihar Kano.
A jawabin ya kara da cewa Khadi Salihu- Muhammad a matsayin Shugaban Hajj da Shehu Tasiu Ishaq a matsayin mabiyi.
Wasu daga cikin masu Sharia sun hada da Hajiya Sakina Yusuf, CSP Adamu Babayo, Musa Zango Mata, yayinda aka tayasu murna da fatan Alheri.