Ganduje Zai Sanya Hannu Da Wani Kamfani A Dubai Domin Gina Makekiyar Kasuwar Zamani A Kano…an ware milyan 500 domin sake fasalin kasuwar Kwari

Gwamnatin jihar Kano zata sanya hannu da wani kamfani na kasar Dubai domin gina makekiyar kasuwa ta zamani a jihar Kano akan kudi Naira Bilyan N500.

Bayanin hakan ya fito ne daga Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a wajen wani taron jin ra’yoyin jama’a na kwana guda da akayi a Kano tare da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Ya ce sun yanke shawarar gina kasauwar ne mai dauke da kayyaki na zamani da shaguna masu dumbin yawa a ciki domin tallafawa yan kasuwa dake shan wahala a tituna wajen tallan kayansu.

HAUSA TIMES ta samu bayani daga Gwamnan cewa a cikin makon nan ne za’a kulla yarjejeniyar kan Naira Biylan 500 domin fara aikin gina kasuwar a farkon sabuwar shekara mai kamawa ta 2017.

Daraktan yada labarai da sadarwa na fadar Gwamnati, Alhaji Salihu Tanko Yakasai yace tuni Gwamnan ya kammala biyan diyya ga wadanda aikin zai shafa.

Gwamnan ya kuma kara da cewa sun ware kimanin Naira Milyan 500 domin sake fasalin kasuwannin jihar ciki harda kasuwar Kwari domin magance saurin kamawa da gobara da kuma rage cinkoso a kasuwannin.

You may also like