Ganduje Zai Yi Katafariyar Gadar Sama A Sha Tale Talen Dangi Dake Kano


DANGI UNDERPASS: Wannan shine zanen sabuwar gada mai hawa uku da Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR zai gina a shataletalen Dangi dake kan titin zuwa Gidan Zoo, aikin zai hada da gadar kasa ga masu wuce wa ko dawo wa akan titin Zaria, sai kuma masu yin kwana a ko wanne sako a doron kasa, sannan sai gadar sama kuma wadda zata taso daga kan titin Gidan Zoo ta sauka a gefen Massallacin Aliyu Ibn Abu Talib.

Wannan aiki dai za’a gina shi ne akan kudi N4Billion kuma ana sa ran fara shi daga wannan wata na March, sannan a kammala shi cikin wata goma In Sha Allah.

You may also like