Yayin da sauran al’ummomi daban-daban na duniya ke amfani da harshe daya tsakanin mata da maza wajen zantuka da mu’amalar yau da kullum, abin ba haka yake ba a garin Ubang na yankin Ƙaramar Hukumar Obudu ta jihar Kuros Riba da ke kudu maso kudancin Najeriya.