An gano mutun na biyu a harin cocin Faransa


 

Masu shigar da kara na gwamnatin Faransa, sun bayyana Abdel Malik Petijean mai shekaru 19 a matsayin daya daga cikin mahara biyu da suka kashe limamin cocin kasar a ranar Talata.

Masu shigar da karar sun ce, shi ma Malik sananne ne ga jami’an tsaro tamkar maharin farko Adel Kermiche.

Jami’an tsaro sun yi nasarar harbe matasan guda biyu bayan sun yi garkuwa da masu ibada a cocin na Saint-Etienne, inda suka kashe limamin cocin, Jacque Hamel mai shekaru 86.

Kungiyar IS mai da’awar jihadi ta fitar da hoton bidiyo, inda ta ikirarin cewa, matasan sun yi mata mubaya’a.

You may also like