Gara Na Mutu Na Shiga Aljannah Na Huta Da Fitinar Yaƙi – Shekau


Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya karyata rundunar sojojin Nijeriya da ke cewa, sun murkushe mayakan kungiyar sa, inda ya ke nuna suna nan da karfin su, kuma baki dayansu sun sadaukar da rayuwar su a wannan yaki da suke yi rundunar bata, a cewar sa.

Shekau wanda ya bayyana a cikin wani sabon faifan bidiyon, ya yi nuni da cewa shi ya gaji da wannan yaki da ake ta kai kawo, burin sa shi ne ya samu shahada, don ya hanzarta shiga Aljanna, a cewarsa.

A cikin sakon bidiyon da aka yi da harshen Hausa mai tsawon minti 10, Shekau ya bayyana matukar takaicinsa kan yadda ake kashe ‘yan kungiyarsa kuma ya ce, hakarsa ba ta cimma ruwa ba, dakarun gwamnati kullum ke samun nasara akan su.

Babu dai alamar karsashi da ya saba nunawa a bidiyon da ya fitar kuma muryarsa na nuna alamun karaya, saboda yadda sojojin Nijeriya ke samun nasara akan ‘yan kungiyarsa.

Wasu ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun fito a matsayin dogaransa a sabon bidiyon, in da suke rike da bindigogi kamar yadda ya saba a kowanne sabon faifai.

Yayi ta kokarin nanata cewa yana nan daram a dajin Sambisa, kuma ya nemi ‘yan kungiyarsa da su zage damtse, don ci gaba da yaki.

Ko menene ra`ayinku dangane da hakan?

You may also like