Garba Isa Ya Yi Ikirarin Cewa Sojoji Ne Suka tilasta Shi Ya Yiwa Shehu Sani Ƙazafi


Dan kato da Goran nan wanda ake zargi da kisan kai a Kaduna, Garba Isa ya yi ikirarin cewa sojoji ne suka tilasta shi kan ya yi wa dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani kazafin cewa yana da hannun wajen kisan kan.

Ya ce ” na shaidawa sojojin cewa Ina daga cikin ‘Yankees kato da gora don haka babu yadda zan kashe wani, daga nan ne, suka fara lakada mani duka kan cewa dole in karba laifin kisan kan kuma cewa Sanata Shehu Sani ne ya umarce mu da yin kisan”.

You may also like