Garba Shehu Yace Beran Dinka Zai Iya Lalata Komai Babban mai taimakawa Shugaban kasa kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu ya dage kan cewar beraye ne sukayi barna a ofishin shugaban kasa Muhammad Buhari inda yace beran dinka zai iya lalata komai.

Garba Shehu ya jawo cece kuce a kwanan baya  lokacin da ya furta cewa beraye ne suka yi barna  ofishin shugaban kasar lokacin da yake jinya a kasar Birtaniya.

Da yake magana da sashen Hausa na gidan rediyon BBC yace wadanda  suka ki gasgata maganarsa kan lalata na’urar samar da sanyi a ofishin shugaban kasar da berayen sukayi, to basu san barnar beran dinka bane.

“Mutane basu san a fada musu gaskiya idan da, bamu fadi gaskiya ba mutane zasu rinka fadin maganganu daban-daban kan  abinda ke faruwa.”

Shehu yace akwai wurin ajiye namun daji da kuma wurare masu ciyawa a fadar shugaban kasa inda daganan beraye zasu iya shiga ofishin.

You may also like