
Asalin hoton, Getty Images
Gareth Southgate zai ci gaba da horar da tawagar Ingila zuwa bayan Gasar Cin Kofin nahiyar Turai ta 2024, in ji hukumar kwallon kafar Ingila.
Tun farko kociyan ya ce bai san makomarsa ba, bayan da aka fitar da Ingila a zagayen daf da na kusa da na karshe a Kofin Duniya a Qatar.
Mai shekara 52, wanda ya karbi aikin kociyan Ingila a 2016 ya kai kasar karawar daf da karshe a Kofin duniya a Rasha a 2018 da wasan karshe a Euro 2021.
Kwantiraginsa zai kare a Disambar 2024
Ya kuma fara jan ragamar Ingila a Nuwambar 2016, bayan wata biyu da ya yi a kociyan rikon kwarya. bayan da Sam Allardyce ya bar aikin.
Southgate ya ci wasa 49 a karawa 81 da ya ja ragamar Ingila da rashin nasara 14.
Tun farko Southagate ya horar da matasan Ingila ‘yan kasa da shekara 21 daga 2013 zuwa 2016, ya kuma yi koci a Middlesbrough daga 2006 zuwa 2009.
A karkashin Southgate, Ingila ta ci kwallo 174 aka zura mata 57 a raga.
Shi ne na hudu a yawan jan ragamar wasannin Ingila a tarihi, bayan Walter Winterbottom mai wasa 139 da Sir Alf Ramsey mai 113 da kuma Sir Bobby Robson da ya ja ragamar wasannin Ingila 95.