Garkuwa da ‘yan sanda ta janyo tarzoma a Armenia


Shugaban kasar Armenia Serzh Sargysgyan ya bukaci ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da jami’an ‘yan sandan kasar da su ajiye makamansu tare da sakin ‘yan sandan.

Wanann na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun kama masu zanga zanga a birnin Yerevan da ke nuna goyon baya ga ‘yan bindigar.

Tun a ranar Lahadin da ta gabata ne, wasu ‘yan bindiga magoya bayan jagoran ‘yan adawar kasar Zhirair Sefilyan da ke kulle a gidan yari, suka yi garkuwa da jami’an ‘yan sandan, inda suka bukaci a saki shugaban nasu wanda aka kama tun a cikin watan Yuni saboda mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Daruruwan Armeniyawa da ke nuna goyan baya ga ‘yan bindigar sun gudanar da zanga zangar ne a kusa da harabar ginin da aka yi garkuwa da ‘yan sandan, abinda ya rikide ya zama tarzoma tsakanin al’umma da kuma wasu jami’ai daban da suka yi wa ginin kawanya.

Jami’an sun tarwatsa jama’ar da hayaki mai sa kwalla tare da kame wasu daga cikin su.
Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce, kimanin mutane 51 da suka hada da ‘yan sanda 25 sun samu raunuka a tarzomar.

A halin yanzu dai, ‘yan bindigar na ci gaba da garkuwa da ‘yan sandan a cikin ginin, amma wasu jami’ai daban sun yi wa ginin kawanya.

Daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su, har da mataimakin ‘shugaban ‘yan sandan kasar, Manjo Vardan Egiazaryan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like