Garkuwan Malaman Zazzau Ya Rasu YauAllah Ya Yiwa Garkuwan Malaman Zazzau Alhaji Mal. Shitu Maloli Aliyu Kusfa Rasuwa, Yau Talata 9/01/2018 A Gidansa Dake Cikin Garin Zaria da Misalin Qarfe 5 Na Subahi. 

Ya Rasu Yana da Shekaru 66 a Duniya, Yabar Mata Hudu (4) da ‘Ya’ya da Kuma Jikoki da Dama. 

anyi Masa Sallar Jana’iza Yau da Misalin Qarfe 2:30 na Rana a Gidansa Dake Low-cost Kusa da Kan Titin Gambo Sawaba General Hospital, Zaria. 

Muna Roqon Allah (SWT) Ya Jiqansa da Rahama, Allah Yasa Mutuwa ta Zamo Hutu da Rahama a Gareshi Alfarman Manzon Allah (SAW).

You may also like