Gasar Hikayata ta mata zalla


Wannan gasa ta mata ce zalla

A karon farko a tarihi sashin Hausa na BBC ya fito da gasar rubutun kagaggen labari ga mata zalla.

Wannan wani yunkuri na bai wa mata damar nuna irin basirar da Allah ya hore musu wurin rubutu da kirkirar labari.

Editan sashin Hausa na BBC Jimeh Saleh, ya ce “a baya mata a nahiyar Afirka sun yi fice wurin bayar da kagaggun labarurruka da kuma tatsuniya da sauransu”.

Sai dai lamarin ya sauya, musamman a kasar Hausa, tun bayan zuwa karatun boko.

Wannan gasa za ta taimaka wurin bunkasa rubutu a tsakanin mata da rage irin gibin da ke tsakaninsu da maza, wanda rashin daidaito wurin samar da ilimi ya haifar.

Yadda za a shiga gasar

Wannan gasa ce ta mata zalla kawai, ko a ina suke a fadin duniya.

Idan kina so ki shiga, sai ki turo mana da kagaggen labarin da ki ka rubuta mai tsawon kalmomi 1000 zuwa 1500.

Za a aika da labarin ne zuwa adreshin labari.bbchausa@bbc.co.uk

Za mu fara karbar sakonni daga ranar 1 ga watan Agusta 2016 sannan a rufe da misalin karfe 23:55 a ranar Juma’a 16 ga watan Satumba.

Ko wacce mace ciki har da kwararrun marubuta na da damar shiga gasar. Mata biyu za su iya hada gwiwa amma banda sama da haka.

Alkalai masu zaman kansu ne za su tantance domin su yanke hukunci.

Za a sanar da wadanda aka zabi labaransu daga ranakun 19 zuwa 22 ga watan Satumba.

Za a gayyato mutane ukun farko da suka samu nasara zuwa wurin bikin bada kyaututtuka da za a yi a Abuja.

 

daga: http://bbchausa.com


Like it? Share with your friends!

0

You may also like