Gasar Share Fagen Cin Kofin Duniya World Cup 2018: Super Eagle Ta Tsallake Rijiya Da Baya


 

A ranar Lahadi Super Eagles ta ci tawagar kwallon kafa ta Zambia 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka kara a Ndola.

Wasan wanda shi ne na farko a rukuni na biyu, ya sa Nijeriya tana mataki na daya a kan teburi, bayan da Algeria da Kamaru suka tashi kunnen doki a ranar ta Lahadin.

Nieriya ta samu nasara akan Zambia duk da isa kasar da ta yi a makare, bayan da shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijeriya Amanju Pinnick ya c e ba su da kudin da za su je wasan.

Rabon da Super Eagles ta ci wasa a waje tun a 2015, bayan da ta doke Congo 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a Pointe Noire.

A shekarar 2017 za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fafata a Gabon, sai dai Super Eagles ba za ta buga wasannin ba, kuma karo na biyu kenan a jere, bayan da kasar ta kasa shiga gasar da aka yi a 2015.
Nasarar da Nijeriya ta yi a Zambia ta karawa ‘yan kasar kwarin gwiwa, bayan da sabon kociya Gernot Rohr da sabbin ‘yan wasan da ya gayyata suka nuna cewar da gaske suke.

Super Eagles wadda ke mataki na 14 a iya murza-leda a Afirka, za ta buga wasan gaba da Algeria wadda ke matsayi na biyu a ranar 12 ga watan Nuwamba a Uyo.

A cikin runkuni na biyu, za a zabi kasa daya da ta fi yawan maki domin wakiltar Afirka daga cikin guda biyar din da za su wakilce ta a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.
Nijeriya ta je wasannin cin kofin duniya sau biyar tun daga shekarar 1994 da 1998 da 2002 da 2010 da kuma 2014.

Kwana daya da samun nasar da kungiyar Super Eagles ta yi akan kasar Zambiya, Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa kungiyar ta Super Eagles, da cewa sun yi namijin kokarin ganin yadda suka shiga har kasar Zambiya kuma suka ci kwallaye biyu suka fito da maki uku.

Ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa  Garba Shehu, inda ya ce; kwazon da kungiyar ta yi a wasan abin a yaba musu ne, idan aka yi la’akari da irin kwazo na tawagar ‘yan wasan ta Zambiya, ganin yadda suka taka rawa a gasar cin kofin nahiyar Afrika da a shekarun da suka gabata.

Ga dukkan alamu a iya cewa dai kungiyar ta Super Eagles ta fara wannan wasa da kafar dama, kamar yadda masu iya magana ke cewa; Juma’ar da za ta yi kyau daga laraba ake ganewa.

You may also like